Laraba 15 Afirilu 2026 - 21:39
Wasikar Godiya Daga Ayatullah Rajabi Kan Matsayar Fafaroma Leo na 14/ Trump Ne Fir'aunan Zamaninmu 

Hauza/ Shugaban Cibiyar Ilimi da Bincike ta Imam Khomeini (RA) ya kuma yi Allah-wadai da cin mutuncin da Trump ya yi wa shugaban Kiristocin duniya, yana gargadin cewa idan mabiyan Annabi Isa (AS) da dukkan mabiyan addinan Ibrahimiyya ba su tashi tsaye ba a gaban girman kai, mulkin kama‑karya da takamar wannan “Fir’aunan zamani”, to su sa ran karin cin mutunci da barazana a gaba.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa Ayatullah Mahmoud Rajabi, memba na Majalisar Koli ta Hauzozin Ilimin Addini a kasar Iran kuma memba na kwamitin shugabanci na Majalisar Kwararru, ya aike da wasika ga Fafaroma Leo na 14 inda ya gode masa kan matsayarsa na yin Allah‑wadai da kashe yara, mata da maza marasa laifi da aka zalunta.

Shugaban Cibiyar Ilimi da Bincike ta Imam Khumaini (R) ya kuma yi Allah-wadai da cin mutuncin da Trump ya yi wa shugaban Kiristocin duniya, yana gargadin cewa idan mabiyan Annabi Isa (AS) da dukkan mabiyan addinan Ibrahimiyya ba su tashi tsaye ba a gaban girman kai, mulkin kama‑karya da takamar wannan “Fir’aunan zamani”, to su sa ran karin cin mutunci da barazana a gaba.

Cikakkiyar fassarar rubutun wasikar Ayatullah Rajabi:

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

إِذْ قالَتِ الْمَلائِکَةُ یا مَرْیَمُ إِنَّ اللَّـهَ یُبَشِّرُکِ بِکَلِمَةٍ مِنْهُ اسْمُهُ الْمَسِیحُ عِیسَی ابْنُ مَرْیَمَ وَجِیهاً فِی الدُّنْیا وَ الْآخِرَةِ وَ مِنَ الْمُقَرَّبِینَ

“Lokacin da mala’iku suka ce: Ya Maryam! Lalle Allah yana yi miki bushara da wata Kalma daga gare Shi, sunansa Almasihu Isa ɗan Maryam; mai daraja a duniya da lahira, kuma yana daga cikin na kusa da Allah.”

Mai Girma Fafaroma Leo na 14 

Da farko ina so in bayyana godiya da yabo kan muhimman kalamanku na yin Allah‑wadai da kisan yara, mata da maza marasa laifi da aka zalunta. Wannan mataki ya yi daidai da koyarwar Allah na babban Annabin addinan Ibrahimiyya, wato Annabi Isa Almasihu (AS).

Kamar yadda kuka sani, Alkur’ani Mai Girma ya yi yabo a ayoyi da dama ga Annabi Isa Almasihu (AS), mahaifiyarsa mai tsarki Maryam (AS), da kuma mabiyansa na gaskiya da Hawariyyai.

Mu a Iran mun shafe shekaru masu yawa muna rayuwa cikin lumana da jituwa tare da Kiristoci masu daraja.

Jagoran juyin juya halin Musulunci wanda ya yi shahada, Ayatullah al‑Uzma Shahid Sayyid Ali Hussaini Khamenei (Q), tsawon shekaru da dama a lokutan Kirsimeti yakan ziyarci gidajen iyalan shahidan Kiristoci don ganawa da su kai tsaye da kuma jajanta musu. A wata hanya ya kasance kamar uba mai tausayi ga dukkan al’ummar Iran, ciki har da mabiyan Annabi Isa, musamman iyalan shahidan Kiristoci.

Shugaban Amurka wanda mutane da dama ke kyama, baya ga kashe mata, yara da maza marasa laifi, tare da hadin gwiwar kungiyar masu laifi ta gwamnatin Sahayoniya, kwanaki 40 da suka gabata ya kashe mafi girman jagoran Shi’awa, har ma na Musulmi baki daya, wanda ya kasance mai nuna kauna ga Kiristoci.

Wannan mataki ba wai kawai barazana ce ga tsarin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba, har ma cin mutunci ne ga dukkan addinan Ibrahimiyya.

Dukkan Annabawa sun hana mabiyansu su zagi ko su tozarta shugabannin sauran addinai. Koyarwar Annabinmu da Annabinku duka suna yin Allah‑wadai da rashin ladabi da cin mutunci ga manyan jagororin addini. Amma abin takaici, shugaban Amurka mai aikata laifuka ya sake yi wa mai girma ku, a matsayinku na shugaban Kiristocin duniya, cin mutunci a fili sau da dama.

Ni kuma ina yin Allah‑wadai da wannan aiki da kakkausar murya, kuma ina gargadin dukkan mabiyan Annabi Isa (AS), har ma da dukkan mabiyan addinan Ibrahimiyya, cewa idan ba mu tashi tsaye ba a gaban girman kai, mulkin kama‑karya da takamar wannan Fir’aunan zamani, to dole mu sa ran karin cin mutunci da barazana a nan gaba. A wannan fanni, Musulmai, Kiristoci da Yahudawan da ke Amurka suna da babban alhaki.

Addinan Ibrahimiyya, musamman malamai na Kirista da Musulmi, za su iya yin hadin gwiwa domin daukar matakan ilimi da aikace‑aikace masu tasiri wajen cimma burinsu na bai daya: wato yada zaman lafiya a duniya da kuma kare wadanda ake zalunta da raunana.

A karshe, ina fata da zuwan mai ceto na karshe — wanda Annabi Isa (AS) ma zai bayyana tare da shi — adalci zai yadu a fadin duniya, kuma zalunci da azzalumai su gushe daga duniya. Insha Allah.

Mahmoud Rajabi

Shugaban Cibiyar Ilimi da Bincike ta Imam Khumaini (R)

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha